Professional Documents
Culture Documents
Sunday, August 29, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 3
Hukuncin Samar da Shugaba a cikin Al’umma
Farilla ce ta kifaya a kan al’umma a samar da shugaba na bai xaya, haka
kuma wajibi ne shugaba ya samar da mataimakansa
Al-Mawardi ya ce:
وعقدىا لمن يقوم بها في األمة واجب باإلجماع ،و شذ عنهم األصم
An-Nawawi ya ce:
وأجمعوا على أنو يجب على المسلمين نصب خليفة ،و وجوبو بالشرع ال بالعقل
Ibn Taimiyyah ya ce:
يجب أن يُعرف أن والية الناس من أعظم واجبات الدين بل ال قيام للدين إال بها
Ibn Taimiyyah ya qara da cewa:
فإن بني آدم ال تتم مصلحتهم إال باالجتماع ،لحاجة بعضهم إلى بعض ،وال بد لهم عند االجتماع إلى أمي ٍر
وقائد يقودىم ،وإذا كان ذلك واجباً في أقل االجتماعات ،وأقصرىا ،فكيف بأمر المسلمين ،وفي ٍ يسوسهم،
الحديث( :إذا خرج ثالثة في سفر فليؤمروا أحدىم) تنبيهاً بذلك على سائر أنواع االجتماعات
Hasanul Bannaa ya ce:
يفترض اإلسالم الحنيف الحكومة قاعد ًة من قواعد النظام اإلجتماعى الذى جاء بو للناس ،فهو ال يُقر الفوضى
وال يدع الجماعة المسلمة بغير إمام
Imam Ahmad ibn Hanbal
البد للمسلمين من حاكم ،أتذىب حقوق الناس
Sunday, August 29, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 4
Dalilan Samar da Shugaba a cikin Al’umma
Ba da tsaro da kariya ga
larurori biyar الضروريات الخمس
Addini
Dukiya
Hankali
Rayuwa
Nasaba da Mutunci
Sunday, August 29, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 8
Siffofin Shugaba da Haqqoqin Shugabanci
Malamai sun bayyana sharuxxa da siffofin shugaba a Musulunci. Amma
kuma sun yi ittifaqi kan cewa idan aka rasa wanda ya dace, dole ne a samu
mai dama-dama ya yi shugabanci.
Al-Ghazaali ya ce:
أو فاسق – وكان في صرفو،لو تعذر وجود الورع والعلم فيمن يتصدى لإلمامة – بأن يغلب عليها جاىل باألحكام
حكمنا بانعقاد إمامتو،عنها إثارة فتنة ال تطاق
Haka nan sun bayyana haqqoqin da shugaba ke da shi a kan mabiya da
haqqoqin da mabiya ke da shi a kansa. A cikin littafin معاملة الحكام, Burjaas ya
yi naqali daga littafin تحرير األحكام في تدبير أىل اإلسالمna Ibn Jamaa’ah Al-Kinaaniy:
Haqqoqin shugaba
Xa’a; nasiha; taimako; kiyaye haqqoqinsa da girmama shi; farkar da gafalarsa;
ankarar da shi game da haxarin makusantar da ke zagon qasa; sanar da shi halin
mataimakansa da wakilansa; haxa kan jama’a; kyakkyawar addu’a; haquri da
shi; da kare martabarsa bisa gaskiya da adalci
Haqqoqin da ke kan shugaba
Tsare martabar musulunci; kare addinin gaskiya; tsai da alamomin Musulunci
( ;)شعائر اإلسالمadalci; tsai da nau’o’in jihadi; xabbaqa Shari’ar Allah; kyautata
duniyar al’umma da kula da dukiyarsu da yin tsuwurwurinta da amfani da ita ta
hanyoyin da suka dace
Sunday, August 29, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 9
Halin da Shugabanci ke Ciki a Yau
Nazari game da yadda shugabanci ya ke a yau na nuna abubuwa guda
biyu: shugabanci a tsakanin Musulmi ko sauran qungiyoyin addini; da
kuma shugabanci na bai xaya a tsakanin jama’ar qasa.
Babu cikakken jagoranci a tsakanin Musulmin Nijeriya, hatta a mataki
na qungiyoyi ko masu bin aqidodi mabambanta, illa iyaka wasu sun fi
wasu dama-dama
A qasa baki xaya kuma, al’amarin shugabanci ya shiga cikin
mawuyacin hali: rashin daular Musulunci da za ta tabbatar wa
al’umma da اخلالفة. Abu mafi haxari kuma a qarqashin wannan matsalar
shi ne rashin ittifaqin malamai a kan hanyar da ta fi dacewa wajen
dawo da tsarin shugabanci na Musulunci. Waxansu ma suna ganin
cewa mafarki ne kawai tunani a kan اخلالفة.