You are on page 1of 14

MATSAYIN AURE A MUSULUNCI:

NAZARI A KAN MUNANAN XABI’UN


DA AKA QAGO A BIKIN AURE

Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmān


Sashen Koyar da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
+2348026499981 (abellodogarawa@gmail.com)
‫‪GABATARWA‬‬
‫‪ Aure‬‬ ‫‪aya ce daga cikin ayoyin Allah kuma ni’ima ce daga cikin‬‬
‫‪ni’imominSa da Ya yi a kan Manzanni‬‬
‫‪ ‬ومن آياته أن خلق لكم من أنفسكم أزواجا لتسكنوا إليها ‪]Ruum, 30:21[ ...‬‬
‫‪ ‬ولقد أرسلنا رسال من قبلك وجعلنا لهم أزواجا وذرية ]‪[Ra’aad, 13:38‬‬
‫‪ An‬‬ ‫‪shar’anta aure, aka qarfafe shi, kuma aka kwaxaitar da shi‬‬
‫‪ ‬فانكوا ما طاب لكم من النساء مثنى وثالثا ورباعا ‪]Nisaa, 4:3[ ...‬‬
‫‪ ‬يا معشر الشباب من استطاع منكم الباءة فليتزوج‪ ،‬ومن لم يستطع فعليه بالصوم فإنه له وجاء‬
‫]‪[Bukhari da Muslim‬‬
‫‪ ‬تزوجوا الودود الولود؛ فإني مكاثر بكم ]‪[Abu Daawud; Nasaa’i‬‬
‫كرهبانية النصارى [‪]Baihaqi‬‬
‫‪ ‬تزوجوا فإني مكاثر بكم األمم‪ ،‬وال تكونوا َ‬
‫‪‬‬ ‫‪An hana tabattul; kuma barin aure don yi ibada, ya sava wa Sunnah‬‬
‫‪ ‬حديث عثمان بن مظعون فى التبتل وأبى هريرة فى التخصر ]‪[Bukhari‬‬
‫‪ ‬النكاح سنتى فمن رغب عن سنتى فليس منى ]‪[Bukhari‬‬
‫‪Sunday, August 15, 2010‬‬ ‫‪Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria‬‬ ‫‪2‬‬
HUKUNCIN AURE
 Musulunci ya kwaxaitar da yin aure a matsayin aikin ibada da a
ke so; kuma hanyar Annabawa.
 Da yawa daga Malamai na ganin cewa aure a haqqin xaixaikun
mutane yana xaukar xayan hukunce-hukuncen Shari’a guda biyar
(‫)األحكام التكليفية‬: waajib; istihbaab; jaa’iz; makruh; haraam
 Maganar da ta fi qarfi ita ce, aure mustahabbi ne ko da ya ke yana
kai wa matsayin wajibi a kan wanda ke da ikon yin aure, da
xaukar xawainiyar iyali, kuma ya ke tsoron aukawa cikin zina
idan bai yi ba, saboda Hadisin Manzon Allah (SAW):
]Bukhari[ ... ‫ يا معشر الشباب من استطاع منكم البائة فاليتزوج‬
 Wajibi ne a kan al’umma gaba xayanta (‫ )فرض الكفاية‬ta qarfafi
al’amarin aure; ta kare martabarsa; kuma ta sauqaqe hanyoyin
yinsa.
Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 3
MATSAYI/MUHIMMANCIN AURE A MUSULUNCI
Aure ya qunshi qulla qwaqqwarar alaqa a tsakanin namiji da mace,
wadda za ta halatta masu zaman tare a matsayin ma’aura, da kuma
jin daxin juna, bisa niyyar bauta wa Allah (TWT).
Allah (TWT) Ya shar’anta aure a matsayin halattaciyar hanya guda
xaya tilo ta samar da ‘ya’ya da kuma yawaita jama’a a doron qasa,
in ban da hanyar kuyangi/sa xaka.
Ta hanyar aure ne a ke samar da iyali a matsayin babban rukunin
al’ummar Musulmi.
Aure na daga matakan da Shari’ar Musulunci ta bi wajen ba da
kariya ga nasaba da mutuncin al’umma.
Aure na da matuqar muhimmanci a cikin tsarin zamantakewar
al’umma, kasancewar yana kare haqqoqin maza da mata da `ya`ya,
xoriya a kan biyan buqatar xabi’a da sha’awa, da kuma gyara
tunanin mutane da kyautata addinin jama’a.
Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 4
MATSAYI/MUHIMMANCIN AURE A MUSULUNCI
Auren da aka gina shi a kan soyayya da qauna, da girmamawa da
mutunta juna, da kyautatawa na ba da gagarumar gudummuwa wajen
tabbatuwar al’umma da inganta al’amuranta.
Wannan ya sa Musulunci ya qarfafi aure kuma ya xauki matakan
dawwamar da shi ta hanyoyin: fifita addini da kyakkyawar xabi’a a
wajen zaven miji/mata; halatta kallon wadda a ke son a aura domin
kada a yi kitso da qwarqwata; sharxanta yardar wadda za a aura,
matuqar ta balaga; hana wa miji neman kamala daga wajen matarsa,
da bayyanar da muhimmancin yin haquri da juna; halatta wa mutane
shiga cikin al’amarin ma’aura domin yin gyara da sulhu a
tsakaninsu, idan akwai buqatar haka; halatta qarya (ba yaudara ba) a
tsakanin ma’aura domin zamantakewa ta qara danqo; da wajabta wa
ma’aurata zamantakewa kyakkyawa a tsakaninsu, ta hanyar bayyana
wa kowannensu haqqoqinsa, da kuma haqqoqin da ke kansa.
Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 5
ME YA SA A KE YIN AURE?
Manufofi da Fa’idodin Aure

Manufofi Fa’idodi

Xa’a ga Allah (TWT) da Manzon Allah (SAW)


 Samun ladan ciyarwa
Xorewar jinsin xan Adam
 Kamewa daga zina da tsare mutunci
Biyan buqatar sha’awa ta xabi’a
Amfana daga addu’ar xa na qwarai bayan mutuwa
Samun natsuwa da sukuni
Samun ladan tarbiyya da xaukar xawainiyar `ya`ya
Samar da iyali da yawaita al’umma
Dacewa da abin da Manzon Allah (SAW) ke so
Samun kamala a cikin al’umma
Raya Sunnar Annabawa
Dacewa da taimakon Allah saboda kange kai

8/15/2010 A.B. Dogarawa, A.B.U., Zaria 6


ABUBUWAN HANI WAJEN NEMAN AURE
Rashin kiyaye sharuxxa da rukunan da Shari’a ta tanada
game da aure
Kaxaituwa tsakanin saurayi da budurwa wajen
zance/hira ko zuwa unguwa ba tare da muharrami ba
Tava wadda a ke nema ko rungumemeniya ko sumbantar
juna
Maganganun da ba su dace ba a kan waya ko yanar gizo
Aikawa da saqonnin batsa ko hotunan tsiraici
Mu’amalar ma’aura don kawai an sanya rana/baiko tun
kafin xaura aure

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 7


AL’ADUN DA AKA SHIGAR CIKIN AURE
Qin neman iznin waliyyai kafin a fara magana

Gaisuwar uwa da uba da kayan baiko/sanya rana


Credit
Kallafawa mai neman aure zuwa gaishe da dangi
Al’adu
Amfani da zoben sanya rana

Kallafa wa kai buga katin gayyata

Ashobe/kayan anko

Sanya kayan coci da yanka cake a lokacin biki


Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 8
AL’ADUN DA AKA SHIGAR CIKIN AURE
Yi wa motar Ango/Amarya adon flower

Abincin bikon Amarya


Credit
Kayan qawayen Amarya
Al’adu
Tsanantawa wajen motocin xaukar Amarya

Tilasta kwana a gidan Amarya bayan an kai ta

Buxen kai

Kayan sayen baki


Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 9
ILLOLIN QAGO AL’ADU A CIKIN AURE
Yawan `yan mata da zawarawa a cikin al’umma saboda rashin
waxanda za su iya yin abubuwan da a ka tsawwala a cikin aure.
Xaukar aure a matsayin wata al’ada da ta shafi haxuwar mace
da namiji don kawai biyan buqatar sha’awar rai.
Rashin qimanta aure a matsayin ibada, da kuma qin la’akari da
manufar Shari’a game da aure.
Jawo wa addini raini da gori a idon waxanda ba Musulmi ba, da
kuma dakushe hasken kevantacciyar karantarwar Musulunci da
tsarinsa na rayuwa.
Kamanceceniya da waxanda ba Musulmi ba a cikin waxansu
al’adun.
Yawan matuwar aure.
Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 10
MUTUWAR AURE A CIKIN AL’UMMA
Rashin fahimtar manufar aure a Musulunci
Auren dole
Rashin tattaunawa a tsakanin ma’aura
Talauci da sauran matsalolin rayuwa
Rashin ba da muhimmanci ga rayuwar aure
Canjin tunani game da abokin zama
Rashin samun yadda a ke zato daga abokin zama
Rashin kula da haqqoqin aure
Ha’intar abokin zama, da rashin kamun kai

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 11


MUTUWAR AURE A CIKIN AL’UMMA
Shaye-shayen barasa ko abubuwan da ke gusar da hankali.
Cin mutuncin abokin zama, ko wulaqanta surukai.
Yawan duka ko zagi.
Rashin sanya ido daga iyaye ko kuma rashin tarbiyya tun
daga gida, kafin aure.
Rashin sanin hanyoyin warware matsala idan ta auku.
Rashin agaji daga al’umma.
Son kai, ko bin son zuciya a tsakanin ma’aura.

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 12


MAGANCE MATSALAR MUTUWAR AURE
Neman yardar Allah
Qoqarin sauke nauyi Gudanar da rayuwa yadda ta ke

Ikhlaas
Koyi da Magabata
Kiyaye Shari’a
Fahimtar manufa Haquri

Qoqarin faranta wa abokin zama rai

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 13


KAMMALAWA
A yau, rayuwar aure na cikin matsanancin hali, kuma tana
fuskantar qalu-bale daga cikin gida da waje. Hakan ya sa
al ’amarin aure ya ke tangal-tangal, kuma da yawa mutane ba su
kai wa ga cinma manufar da ta sa Musulunci ya Shar’anta aure.
Akwai buqatar Musulmi su dawo cikin hayyacinsu; su sake
nazari cikin al ’amuransu; su qara fahimtar matsalolin da harkar
iyali ke fuskanta a cikin al ’umma; sannan su ba juna shawarwari
game da hanyoyin magance su.

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 14

You might also like