You are on page 1of 5

Page 1 of 5

MUHIMMANCIN ILMI A RAYUWAR MUSULMI

Ahmad Bello Dogarawa


Shashin Koyar da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
abellodogarawa@gmail.com

Gabatarwa
Ilmi shi ne mafificin abin da ya kamata a yi amfani da dukiya
wajen nemansa, domin kuwa babu abin da ya kai shi daraja. Da ilmi
ne ake sanin Allah domin a bauta maSa; kuma da ilmi ne ake sanin
haqqoqin kowa domin a ba shi. Ilmi haske ne da ake shiryuwa da shi;
yana gadar da taqawa; kuma yana jawo daraja da xaukaka ga wanda
ya mallake shi. Ilmi shi ne ma’aunin halas da haram; kuma shi ne
maganin cutar jahilci da rarraba a tsakanin mutane.
Neman ilmi ibada ce kuma bitarsa tasbihi ne; bincike a kansa
jihadi ne; koyar da shi ga wanda bai sani ba sadaka ce kuma yaxa shi
a cikin masu shi aikin lada ne. Ilmi mai xebe wa mai shi kewa ne a
lokacin kaxaici, kuma aboki ne a halin tafiya; da shi ne ake sanin
Allah kuma a bauta maSa; da shi ne ake sanin matsayin Allah kuma a
girmama Shi.

Ma’anar Ilmi

77
216

Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi – Ahmad Bello Dogarawa, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
Page 2 of 5

142
143
14

120

148

22

167 166

78

83
148

Falalar Ilmi da Kevance-kevancensa


Ilmi haske ne wanda ke nuna wa mai shi bambancin gaskiya da
qarya (Saba’, 34:6); yana gadar da tsoron Allah (Israa, 17:107-109);
shi ne mafificin jihadi (Furqaan, 25:52); alama ce ta masu imani
(Munafiqun, 63:8); ba ya yankewa saboda mutuwa (Saheeh Muslim);
la’ana ba ta sauka a kan ilmi (Tirmidhi); alama ce ta alheri (Baihaqi);
kuma yana shigar da mutane hanyar aljanna (Muslim). Saboda falalar
ilmi, Allah (Mai girma da xaukaka) Ya yi wa Annabi Yusuf da Musa
da Isa da Muhammad (tsira da aminci su tabbata a gare su) gori a kan
Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi – Ahmad Bello Dogarawa, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
Page 3 of 5

ilmin da Ya ba su (Yusuf, 12:22; Qasas, 28:14; Maa’idah, 5:110;


Nisaa, 4:113).
Ilmi ya kevanta da abubuwa guda shida: (1) shi ne gadon
Annabawa (2) shi ne kaxai aka yi wa Manzon Allah (tsira da aminci
su tabbata a gare shi) umurni da yin addu’ar Allah (Mai girma da
xaukaka) Ya qara masa (3) Allah Ya siffanta kanSa da shi (4) kowane
mutum yana farin ciki idan aka danganta ilmi a gare shi, ko da kuwa
ba shi da ilmi; haka nan kowane mutum ba ya son a danganta shi
zuwa ga kishiyar ilmi, ko da kuwa jahili ne (5) shi ne kaxai abin da ba
ya raguwa daga mai shi saboda ya ba wani (6) ilmi ba ya qarewa
saboda yawan karantarwa, shi yasa ba a tava samun wanda aka ce,
‘Allah sarki, wane ya kasance mai ilmi, amma yanzu ilmin ya qare’,
duk da cewa a kan ce, ‘wane mai kuxi ne, amma yanzu ba shi da
kome’ ko kuma ‘wane mai mulki/sarauta ne, amma yanzu ba shi da
kome’.

Matsayin Masu Ilmi


Malamai su ne ke yi wa al’umma tarbiyya a kan ilmi (Aal
Imraan, 3:79; Maa’idah, 5:44); su ne ke yi wa al’umma shugabanci,
matuqar sun lazimci haquri da taqawa (Baqarah, 2:248; Sajdah,
32:24); suna daga cikin Ulul Amr da aka ce a yi wa xa’a (Nisaa,
4:59); su ne Ahluz Zikr da aka ce a yi wa tambaya (Nahl, 16:43;
Anbiyaa, 21:7); su ne Allah Ya ce a koma gare su a lokacin da wani
abu mai girma ya auku (Nisaa, 4:83); su ne waxanda Allah Ya gwama
shaidarsu da shaidarSa (Aal Imraan, 3:18); su ne waxanda bin
hanyarsu ke kai mutum ga shiriya (Maryam, 19:43); su ne magadan
Annabawa (Abu Daawud da Tirmidhi); su ne waxanda ke tsoron
Allah (Faaxir, 35:28); suna daga cikin waxanda Allah Yake xaukaka
darajarsu (Mujaadalah, 58:11); kuma suna daga cikin waxanda Allah
Yake nufi da alheri (Bukhaari da Muslim); su ne mafi hasken fuska
kuma mafi xaukakar mutane saboda addu’ar Manzon Allah (tsira da
aminci su tabbata a gare shi) gare su (Ahmad, Abu Dawud, Tirmidhi
da Ibn Maajah); Allah (Mai girma da xaukaka) Ya hore masu kome
don ya nema masu gafarar Allah kuma ya yi masu addu’a (Abu
Ya’alaa); su ne waxanda Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a
gare shi) ya bar wasiyya game da su (Ibn Maajah).

Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi – Ahmad Bello Dogarawa, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
Page 4 of 5

Rabe-raben Ilmi da Hukuncin nemansa


Malamai sun raba ilmi ta hanyoyi dabam-daban. Daga ciki:

Al-Ghazaalee ya raba ilmi gida uku bisa waxansu ginshiqai kamar


haka:
1. Asali: saukakke/wanda aka yi wahayinsa (wanda aka koya
daga Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da
wanda ba saukakke ba (amma ana samunsa ta hanyar zurfafa
tunani ko gogayya ko saurare, kamar lissafi da ilmin likitanci
da ilmin harsuna)

2. Hukuncin nemansa: wajibin kowa da kowa (yadda za a bauta


wa Allah da kyawawan xabi’u da sanin ya kamata) wajibin
al’umma baki xaya (noma, likitanci, harhaxa magunguna,
zane-zane, da kimiyya da fasaha)

3. Matsayi: wanda ake buqata, da wanda aka halasta da wanda


aka haramta

A cikin littafin ar-Rasool wal Ilm Qaradawi ya raba ilmi zuwa


1. Ilmin Shari’ah
2. Ilmin sana’a
Neman ilmin Shari’ah domin yin abin da Allah Ya xora wa
kowane bawa wajibi ne (Nahl, 16:43; Anbiyaa, 21:7; Muhammad,
47:19; Xabaraani); idan kuwa na kowa da kowa ne, wajibi ne a kan
al’umma gaba xayanta (Ibn Abdil-Barr; An-Nawawi; Ibn Taimiyyah).
Haka nan ma neman ilmin sana’a da kimiyya da fasaha da sauran
na’o’in ilmin rayuwa, wajibi ne al’umma ta samu wakilci saboda
(Anfaal, 8:60) da kuma qa’idar

Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi


o Da ilmi ne ake tabbatar da tsantsar bauta ga Allah
o Sanin halas da haram
o Sanin kevance-kevancen Musulunci da falalarsa
o Tunkarar qalubalen da ke fuskantar al’umma (munanan aqidodi;
al-gazwul fikriy, koma bayan Musulmi a fagen ilmi da tattalin
arziqi da gudanarwa, da sauransu)
o Kyakkyawan wakilci ga Musulmi a kowane vangare na rayuwa
Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi – Ahmad Bello Dogarawa, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
Page 5 of 5

o Bin umurnin Allah (Mai tsarki da xaukaka) da ManzonSa (tsira da


aminci su tabbata a gare shi)

Wane Ilmi za a Fara Nema?


 Tauhid, sa’an nan yadda za a bauta wa Allah
 Alqur’ani da Hadisi da maganar Malamai (Sahabbai da Tabi’ai)
 Littafan Fiqh
 A haxa su shi ne ya fi

 A vangaren fiqh, a koya ta hanyar mazhaba bisa sharuxxa guda


uku: (i) bin mazhaba da yin fice wurin nemanta ba wajibi ba ne,
kuma ba sharaxi ba ne; (ii) rashin ta’assubanci ga mazhaba; (iii)
wajibcin riqo da dalili sahihi ko da ya sava wa mazhaba
[Duba da na Shaukaaniy; da
na Muhammad Eid Abbaasiy

Ladubban Neman Ilmi


 Tsarkin zuciya da ikhlasi (nisantar shagala da kafin , da ba
da fatawaba tare da tsoro ba, da son jayayya, da kutsawa cikin
, d kallon banza ga wanda ya sava)
 Mayar da himma da tsayar da tunani wuri xaya, da haquri da kaxan
da dauriya, da addu’a, da nisantar savon Allah, da yin aiki da ilmi
 Qanqan da kai ga ilmi da malamai
 Tsare haqqoqin malami (voye sirri, da rashin gulma, da rashin
shiga sai da izni, da ba shi lokacin hutu)
 Yin ado da ladubba majlisi
 Ladabin tambaya
 Bi sannu-sannu kuma mataki-mataki
 Rashin dogaro da littafi ba tare da malami ba
 Rashin koyon karatu daga wanda bai qware ba

Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi – Ahmad Bello Dogarawa, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria

You might also like